Connect with us

News

An Sanya Dokar Hana Zirga-zirga A Adamawa

Published

on

images (8)

Gwamnatin jihar Adamawa ta ayyana dokar ta baci ta hana zirga-zirgar mutane na tsawon sa’o’i 24 a karamar hukumar Lamurde da ke kudancin jihar, bayan samun rahotannin mutuwar kimanin mutane hudu a wani sabon rikici na kabilanci.

Kazalika kwamishin ‘yan sandan jihar Dankombo Morris ya kaddamar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin, tare kuma da jibge ‘yan sandan kwantar da tarzoma a yankin na Lamurde domin tabbatar da doka da oda.

Advertisement

NNPP Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Birni Da Mataimakinsa

Ko a farkon wannan wata na Yuli da muke ci, an samu tashin hankali a kauyukan Lafiya da Boshikiri da ke kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar ta Adamawa.

 

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending