News
Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haddasa Ambaliya A Barcelona
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya a wasu yankunan arewa maso gabashin Spain tare da kawo tseko ga zirga-zigar jiragen sama da na kasa.
Mutane akalla biyu sun yi batan dabo a yankin Kataloniya da ke arewa maso gabashin Spain, bayan wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tabka da yammacin jiya Asabar.
Masu aiko da rahotannin sun ce mamakon ruwan saman ya haddasa ambaliya a gurare da dama cikin har da wani asibiti da ke Barcelona inda ya haddasa katsewar lantarki, sannan kuma an samu tseko na zirga-zirgar jiragen kasa na tsawon sa’o’i da dama.
Hakazalika a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Barcelona an ba da rahoton cewa wani jirgi da ya tashi zuwa Amurka ya sake dawowa ya sauka sakamakon lalata wasu sassansa da kankara ta yi.
Baya ma ga yankin Kataloniya, wasu yankuna da dama a arewa maso gabashin Spain din sun fuskanci mamakon ruwan saman, ciki har da Aragon da Valencia inda tuni aka tura rundunonin jami’an ceton gaggawa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
