News
Yadda Farashin Taki Ke Zama Barazana Ga Harkar Noma
Wasu manoma a jihar Kano sun bayyana jin daɗinsu kan saukar da aka samu a farashin shinkafa, sai dai sun koka da hauhawar farashin taki da ke barazana ga harkar noma, musamman ga manoman da ke da ƙaramin ƙarfin tattalin arziki.
A wata tattaunawa da NIGERIAN TRACKER, wani manomi a garin Danhassan da ke Karamar Hukumar Kura, mai suna Aminu, ya ce yanzu haka farashin shinkafa ya ragu sosai idan aka kwatanta da bara.
SERAP Tayi Karar NNPC Kan zargin wawure Naira biliyan 825 Da Dala Biliyan 2.5
“Yanzu haka, ana sayar da shinkafar girki a kan Naira 2,500 a mudu, yayin da irin shinkafar da ake amfani da ita wajen yin tuwo ke kai Naira 2,900,” in ji Aminu.
Ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata, wadannan nau’o’in shinkafa na kai tsakanin Naira 4,000 zuwa Naira 4,200 a mudu, wanda hakan ya tilasta wa jama’a da dama rage yawan cin shinkafa.
Sai dai ya ce duk da saukin farashin shinkafa, akwai matsanancin ƙalubale wajen samun taki saboda hauhawar farashinsa da ke kara ta’azzara.
“A da ana samun buhun takin Urea a kan Naira 35,000, amma yanzu ya kai Naira 40,000. Takin NPK kuwa, yanzu ana sayar da shi tsakanin Naira 55,000 zuwa Naira 58,000, bisa la’akari da nau’in taki da kuma yankin da ake sayar da shi,” in ji shi.
Aminu ya ce wannan hauhawar farashi na taka wa manoma burki, musamman ƙananan manoma da ke kokarin ci gaba da noma duk da matsanancin yanayin tattalin arzikin da ƙasar ke ciki.
Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta kawo dauki cikin gaggawa ta hanyar bayar da tallafi ko rage haraji a kan takin zamani domin sauƙaƙa wa manoma gudanar da ayyukansu.
“Idan aka bar farashin taki ya ci gaba da hawa, manoma da dama ba za su iya shiga gonaki ba, wanda hakan zai iya haddasa karancin abinci da tsadar kayan masarufi a kasuwa,” in ji shi.
