News
JAMB Ta Zargi Ɗalibin Da Ya Fi Kowa Hazaƙa A 2025 Da Aikata Ha’inci
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu a Najeriya (JAMB) ta bayyana zargin cewa ɗalibin da ya fi kowa samun maki a jarrabawar bana ya aikata ha’inci.
Matashin da ake magana a kansa, Chinedu Okeke, wanda ya fito daga jihar Anambra, ya samu maki 375 cikin maki 400 a jarrabawar UTME da aka gudanar a shekarar 2025.
Okeke dai ya nemi gurbin karatu ne a sashen Injiniya na Jami’ar Legas (UNILAG), amma hukumar JAMB ta ce ya saba doka.
Shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce Okeke ɗalibi ne da ke aji huɗu a sashen koyon Likitanci a Jami’ar Nsukka (UNN), wanda hakan ke nuni da cewa bai kamata ya sake rubuta jarrabawar ba.
“Mun tuntuɓi jami’ar, kuma sun tabbatar mana cewa Okeke ɗalibi ne mai hazaka a aji na huɗu,” in ji Oloyede.
Zargin da JAMB ke yi ya jawo ce-ce-ku-ce a dandalin sada zumunta, inda jama’a da dama suka nuna rashin amincewarsu da matakin hukumar.
Shugaban kamfanin Educare, Alex Onyia, ya bayyana cewa Chinedu ya bi duk dokokin da JAMB ta shimfiɗa, kuma babu wani laifi da ya aikata.
Ya ce, “Akwai matsala wajen daidaita bayanan NIN da JAMB tun shekarar 2021, amma bayanan an riga an gyara su kuma an aike da su ga JAMB.”
Onyia ya ƙara da cewa, “Na yi magana da iyayensa, kuma babu wata hujja da ke nuna cewa Okeke ya aikata wani laifi.”
A wata sanarwa da mai magana da yawun JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya fitar, hukumar ta ce tana amfani da bayanai masu tushe daga NIMC.
“Bayanan da muke da su sun nuna cewa Okeke ya fito ne daga ƙaramar hukumar Amuwo-Odofin a Jihar Legas, ba daga Anambra ba,” in ji Fabian.
JAMB ta ce matashin ya samu gurbin karatu a fannin koyon Likitanci a UNN a 2021, kuma yanzu haka yana aji na huɗu.
Ta ƙara da cewa da zarar an tabbatar da cewa ba ɗalibi ba ne a jami’ar, za ta bukaci Hukumar Kula da Likitoci ta goge sunansa daga tsarin karatu.
“Sai bayan samun tabbaci za mu ɗauki matakin hukuma. Amma a yanzu, har yanzu shi ɗalibi ne a hukumance,” in ji hukumar.
Lauyan Okeke ya bayyana cewa an samu matsala ne tun 2021 a lokacin da aka fara buƙatar amfani da NIN wajen rajistar UTME.
Ya ce, “Bayan an gyara bayanan a wancan lokacin, an aike da takardar gyaran zuwa ga JAMB.”
Amma hukumar JAMB ta musanta wannan zargi.
“Ba mu sauya ko ƙara wani bayani daga hannun ɗalibi ba. Wannan ƙoƙari ne na yin ƙarya da kariya,” kamar yadda sanarwar JAMB ta ƙara jaddadawa.
Yayin da aka fara samun ƙarin martani daga ɓangarorin daban-daban, jama’a na sa ido kan matakin da JAMB za ta ɗauka kan Chinedu Okeke.
Masana harkar ilimi da jama’a na kira da a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya da adalci a lamarin da ya ja hankalin ƙasa baki ɗaya.
