Connect with us

News

RASUWAR BUHARI: Gwamnati Ta Ayyana Litinin A Matsayin Ranar Hutu

Published

on

Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana Litinin, 14 ga Yuli, 2025, a matsayin ranar hutu domin girmama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin London yana da shekaru 82.

‎Sanarwar ayyana ranar hutun na musamman na ƙunshe ne a cikin wata takarda da Sakatare Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya sanyawa hannu a madadin Gwamna Dikko Umaru Radda.

Advertisement

JAMB Ta Zargi Ɗalibin Da Ya Fi Kowa Hazaƙa A 2025 Da Aikata Ha’inci

‎A cewar sanarwar, wannan rana ta hutu na da nufin bai wa al’umma damar yin jimami, tunani da kuma addu’o’i domin rahamar Allah ga marigayi shugaba Muhammadu Buhari.

‎Gwamna Radda ya bayyana marigayi Buhari a matsayin “shugaba nagari, gwarzo, ɗan dimokuraɗiyya na gaskiya da dattijo mai kishin ƙasa wanda rayuwarsa gaba ɗaya ya  sadaukar da kai  ga hidimar Najeriya.”

Advertisement

“Mun yi rashin gwarzon da sunansa ya zamo tamkar alamar ɗa’a, gaskiya da sadaukarwa ga ƙasa. Ina roƙon Allah (SWT) Ya gafarta masa, Ya kuma ya Aljannatul Firdaus ta zama makuma,” in ji Gwamna Radda‎

‎Marigayi Buhari, ɗan asalin garin Daura da ke Jihar Katsina, ya shugabanci Najeriya a matsayin Shugaban Ƙasa na mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan ya sake dawowa kan mulki a matsayin Shugaban Ƙasa na dimokuraɗiyya daga 2015 zuwa 2023.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending