News
“Rasuwar Buhari: Ƙasar Nan Ta Yi Babban Rashi – In Ji Kano Online Media Chapel”
Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo na Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Kano wato Kano Online Media Chapel, ta bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi, ba ga Najeriya kaɗai ba, har da nahiyar Afirka gaba ɗaya.
Sanarwar da shugaban ƙungiyar, Abdulkadir Abubakar Dangambo, tare da sakataren ƙungiyar, Isiyaku Ahmed, suka sanya wa hannu, ta ce rasuwar tsohon shugaban ƙasa a London ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, ta bar babban gibi a tarihin mulkin ƙasa da tafiyar da shugabanci mai cike da gaskiya da rukunin amana.
RASUWAR BUHARI: Gwamnati Ta Ayyana Litinin A Matsayin Ranar Hutu
“Buhari ya rayu ne da gaskiya, ya yi shugabanci mai sauƙi, yana da kishin ƙasa da sadaukarwa wajen ganin Najeriya ta zauna lafiya kuma ta bunƙasa,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta Kano Online Media Chapel ta ce marigayin ya bar tarihi mai cike da darussa ga shugabannin yanzu da na gaba, kasancewar shugabancinsa ya tsaya kan tubalin rikon amana da tsare martabar ƙasa a duniya.
“A matsayin soja da shugaban ƙasa na farar hula, Buhari ya nuna jarumta da kishin ƙasa, musamman a fagen yaƙi da cin hanci da rashawa da ƙarfafa tsaro da tsabtace shugabanci,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma mika ta’aziyyarta ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Katsina, iyalan marigayin da daukacin al’ummar Najeriya bisa wannan babban rashi.
“Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya ba shi Aljanna Firdaus, tare da bai wa iyalansa, ‘yan’uwansa da al’ummar Najeriya haƙurin jure rashin da aka yi.”
Sanarwar ta ce Buhari ya kasance jagora da ake koyi da shi, kuma abubuwan da ya bari za su ci gaba da haskaka tafarkin shugabanci nagari a ƙasar nan.
