News
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 1,111, Sun Yi Garkuwa Da 276 A Cikin Wata Ɗaya — Rahoto
Wani sabon rahoto da kamfanin tsaro da leƙen asiri, Beacon Security and Intelligence Limited, ya fitar ya bayyana cewa mutane 1,111 ne suka rasa rayukansu, yayin da 276 aka yi garkuwa da su a faɗin Nijeriya a watan Yuni 2025 sakamakon hare-haren ƴan bindiga da wasu ƙungiyoyi masu ɗaukar makami.
Rahoton ya nuna cewa an samu raguwa a yawan hare-haren tsaro idan aka kwatanta da na watan Mayu 2025, inda aka samu saukar kashi 48.04% daga hare-hare 895 a Mayu zuwa 465 a Yuni. Haka zalika, yawan mace-mace ya ragu da kashi 14.27%, daga 1,296 zuwa 1,111. Garkuwa da mutane ma ta fadi da kashi 74.59%, daga 1,086 zuwa 276.
Akalla Kauyuka Biyar Ne Suka Tsere Daga Gidajensu Sakamakon Harin Ƴan Bindiga A Neja
Rahoton ya nuna cewa mafi rinjayen adadin wadanda suka mutu fararen hula ne, da suka kai kashi 72.37% na wadanda rikicin ya shafa. Rikicin manoma da makiyaya, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya, na daga cikin manyan dalilan asarar rayuka.
A bangaren garkuwa da mutane kuwa, Arewa maso Yamma ce ta fi fama da lamarin da kashi 72.10% na wadanda aka yi garkuwa da su a fadin kasar.
Jihar Zamfara ce ta fi fuskantar hasarar rayuka da garkuwa da mutane a watan Yuni, inda rahoton ya ce mutum 1,088 ne suka mutu, yayin da fiye da 1,755 aka yi garkuwa da su a jihar.
Kazalika, rahoton ya yi nazari kan watanni uku na baya-bayan nan, inda aka gano cewa tashin hankali ya ragu da kashi 1.95%, amma yawan mace-mace ya karu da kashi 5.66%, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya.
Daga watan Janairu zuwa Yuni 2025, jimillar mutane 6,800 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikice-rikicen tsaro a faɗin ƙasar, abin da ke nuni da ƙarin kashi 19.11% idan aka kwatanta da rabin shekarar farko ta 2024.
Rahoton ya kara da cewa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na ci gaba da fuskantar barazanar ayyukan ƴan ta’adda, yayin da Arewa ta Tsakiya ke ci gaba da fama da rikicin manoma da makiyaya, musamman a jihohin Neja, Benuwe, Filato da Kwara.
