News
Gwamnan Bauchi Ya Karbi Bakoncin Bukola Saraki Da Tambuwal
Daga mujahid danlami garba
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya karbi bakuncin takwaransa na jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da shugaban majalisar dattawa ta 8, Abubakar Bukola Saraki da tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau.
Da yake jawabi yayin ganawar tasu Sanata Saraki ya ce sun kawo ziyara jihar Bauchi ne domin tattaunawa da Gwamnan Bala Abdulkadir da sauran masu neman takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP daga yankin Arewa.
Tattaunawar kokarin lalubo hanyoyin da za a bi ne domin kyautata rayuwa ‘yan Najeriya da kuma samar da kyakkyawar makoma ga jamiyyar da kuma yan jam’iyyar PDP Baki daya.
A cewar Saraki, jam’iyyar PDP, ita ce jamiyya daya tak, da take da tsare tsare na hanyar inganta rayuwar yan Nijeriya da samar musu mafita da ta dace da su.
PDP jam’iyya ce mai tsari ingantacciya da zata iya samar wa ‘yan Nijeriya kyakkyawan shugabanci ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da hadin kan ƙasar mu Nijeriya.
Ya kara da cewa duk masu neman shugabancin kasar nan daga jam’iyyar PDP mutane ne masu matikar muhimmanci da suka damu da halin da kasar nan ke ciki da kuma wahalhalun da gwamnatin APC ta haifar don haka akwai bukatar a hada kai a kawo dauki ma Kasar mu Nijeriya.
