News
Farfesa Gwarzo ya gwangwaje makarantar Intercontinental Schools da sabuwar mota mai kujera 30
Shugaban Rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ba da bababr mota mai kujeru 30 ga Makarantar Intercontinental Schools da ke Kano.
Farfesa Gwarzo ya sanar da wannan kyauta ne a lokacin bikin Ranar Jawabi da Rabon Kyaututtuka na makarantar da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga Yuli, 2025.
Ya ce wannan kyauta na nuna girmamawa ne ga bajintar makarantar wajen fannin ilimi, yana mai jaddada cewa makarantar na daga cikin manyan makarantun sakandare mafiya kyau a jihar Kano.
Farfesa Gwarzo ya shawarci shugabannin makarantar da su mayar da hankali wajen kirkire-kirkire domin bunkasa tunani mai zurfi a tsakanin dalibai, domin iya fafatawa a kalubalen rayuwa a nan gaba da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban jihar da Najeriya baki daya.
“Ilmi shi ne gaba, kuma gaba shi ne ilmi. Idan ka ba wa ‘ya’yanka ingantaccen ilimi, kana saka hannun jari ne a makomarsu,” in ji shi.
Haka kuma, ya bukaci makarantar da ta fara koyar da harshen biyu domin samar da daliban da za su iya aiki a ko’ina cikin duniya ba tare da wata tangarda ba.
Farfesa Gwarzo ya kuma sanar da bayar da kyaututtukan kudi ga fitattun daliba kamar haka, inda wadanda suka zo na farko daga matakin Nursery, Primary da Secondary suka samu kyautar Naira Miliyan Daya kowannensu, sai wadanda suka zo na biyu da na uku suka samu Naira Dubu Dari Biyar kowannensu.
A jawabansu na ban girma daban-daban, shugabannin makarantar Injiniya Yusuf Baba da Hajiya Hadiza Nuhu Yusuf Baba sun yaba wa Farfesa Gwarzo bisa yadda ya nuna kulawa da goyon baya ga makarantar.
Haka kuma sun nuna godiya bisa gudunmawar motar da ya bayar wacce a cewarsu za ta taimaka matuka wajen bunkasa harkokin koyarwa dazirga-zirgan dalibai a makarantar.
Makarantar ta karrama Farfesa Gwarzo da kyautar yabo bisa kokarinsa na musamman wajen bunkasa ilimi a Najeriya da ma kasashen waje.
Cikin wadanda suka raka Farfesa Gwarzo daga jami’ar sun hada da Shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, Mataimakin Shugaban Jami’a kan Harkokin Gudanarwa, Dr. Habib Awais Abubakar, da Mataimakin Shugaban Jami’ar MAAUN Niger, Dr. Shu’aibu Tanko.
Sauran sun hada da Dekan Makarantar Digiri na Biyu, Farfesa Ahmad Maigari Ibrahim, Daraktan Cibiyar Bincike da Kirkire-Kirkire a Harkar Ilimi ta Afrika (IAHERI), Farfesa Abubakar Sadiq Haruna, Mataimakin Shugaban Jami’a kan Harkokin Dalibai, Dr. Hamza Garba da Dr. Bala Mohammad Tukur, Darakta na Harkokin Hulda da Hadin Gwiwa, da sauransu.
