Connect with us

News

Al’ummar Tsamiya Babba Bakin Rafi Sun Nemi Daukin Gaggawa Daga Gwamnatin Kano

Published

on

1753072394026

Al’ummar yankin Tsamiya Babba Bakin Rafi da ke cikin Karamar Hukumar Gezawa a Jihar Kano sun roƙi Gwamnan Jihar,Abba Kabir Yusuf, da kuma Shugaban Karamar Hukumar Gezawa da su gaggauta kai musu dauki, sakamakon matsanancin halin da suka shiga na matsalar zaizayar kasa da rugujewar gine-gine a yankin.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin, Malam Abdulrazaq Ali, ya bayyanawa FREEDOM RADIO cewa  lamarin ya kai wani matsayi na ban tsoro, inda ya ce gidajen mutane da dama na fuskantar barazanar ruftawa a duk wani lokaci.

Advertisement

“Rayuwarmu na cikin haɗari. Za mu iya rasa gidajenmu, hatta rayukanmu, muddin ba a kawo mana agajin gaggawa ba,” in ji Malam Abdulrazaq cikin damuwa.

Ya ƙara da cewa matsalar zaizayar kasar na ci gaba da ruftawa lokaci zuwa lokaci, musamman a darare, lamarin da ke tilasta wasu daga cikin mazauna yankin barin gidajensu su kwana a waje domin tsira da rayuka.

Advertisement

Sun kuma nemi shugabannin al’umma, ‘yan majalisar dokoki da ke wakiltarsu, da su sa baki don ganin gwamnatin jiha da ta ƙaramar hukuma sun tashi tsaye wajen ceton rayuka da dukiyoyi.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da damina ke tsaka da gudana a fadin Jihar Kano, wanda ke haifar da matsaloli iri-iri musamman ga yankunan karkara da ke fama da matsalar zaizayar kasa da ambaliya.

Advertisement

Gwamnatin Kano da ta Karamar Hukumar Gezawa dai har zuwa yanzu ba su fitar da sanarwa ba kan lamarin, sai dai al’umma na ci gaba da sa ran samun kulawa cikin gaggawa daga mahukunta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending