Connect with us

News

Farfesa Adamu Gwarzo Ya Samu Lambar Girmamawa Daga Jaridar Blueprint Kan  Bunkasa Ilimin Jami’a A Najeriya 

Published

on

FB IMG 1753229355478

Shugaban kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya samu lambar yabo ta musamman daga jaridar Blueprint, wadda ta karrama shi da lambar Trailblazer in Tertiary Education – wato gwarzon da ya fi taka rawa wajen bunkasa ilimin gaba da sakandare a Najeriya.

An mika masa wannan karramawa ne a wani biki na musamman da aka gudanar a ranar Talata, 22 ga Yuli, a birnin tarayya Abuja, inda manyan ‘yan siyasa, shugabannin kamfanoni, da fitattun jami’ai daga fadin Najeriya suka halarta.

Advertisement

Majalisar Dattawa Ba Ta Amince Da Kirkiro Sabbin Jihohi Ba — Akpabio

A yayin bikin, an bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin ɗaya daga cikin fitattun gwarazan da suka canza fuskar ilimin jami’a a Najeriya da ma nahiyar Afirka. An jaddada cewa karkashin jagorancinsa, rukunin jami’o’in MAAUN sun zama ginshiƙi wajen bayar da ingantaccen ilimi da horo na zamani, tare da haɗin gwiwa da manyan jami’o’in duniya.

Baya ga wannan lamba, Farfesa Gwarzo ya riga ya samu wasu lambobin yabo na kasa da kasa, ciki har da Award of Excellence daga Cité Internationale Universitaire de Paris, Mbeki Leadership Award, da kuma QAHE Honorary Fellowship, saboda jajircewarsa wajen inganta tsarin ilimi da gina alaka tsakanin jami’o’in Najeriya da sauran duniya.

Advertisement

A jawabinsa na godiya, Farfesa Gwarzo ya ce “Wannan lambar yabo ba wai tawa ba ce kawai, amma ta dukkan matasan Afirka da ke da yakinin cewa ilimi shi ne mafi ingancin makami na kawo sauyi. Za mu ci gaba da karya tudu, gina gadar ilimi, da zuba jari a makoma ta hanyar ilimi.”

A yayin taron, wasu fitattun shugabanni da masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban suma an karrama su. Sanata Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Dattawa, ya samu lambar Dan Siyasa na Shekara, yayin da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya karɓi Mutumin Shekara. Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya samu lambar Excellence in Security Synergy.

Advertisement

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar Gwamnan Shekara a Fannin Ilimi, yayin da takwaransa na Kaduna, Uba Sani, ya karɓi lambar Gwamnan Shekara a Tsaro da Zaman Lafiya. Sanata Barau Jibrin ya lashe lambar Sanata Mafi Fice na Shekara, sai kuma wasu gwamnoni daga jihohin Sokoto, Kebbi, Kogi, Anambra da Katsina da suma aka karrama.

Shugaban BUA Group, Abdulsamad Rabiu, ya samu lambar yabo kan gudummawarsa ga masana’antu da ayyukan jin kai.

Advertisement

Taron ya kasance wani dandali na karrama jajirtattu da ke sauya al’umma, tare da nuni da muhimmancin jagoranci na gari, da himma wajen inganta rayuwar jama’a, musamman a bangaren ilimi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending