Connect with us

News

Ambaliya Ta Halaka Mutane 165, Yayin Da Wasu 82 Suka Bace A Bana – NEMA

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa akalla mutane 165 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 82 suka bace, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a sassa daban-daban na ƙasar nan a cikin wannan shekarar.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton kididdiga da ta fitar a ranar Juma’a, wanda ya fayyace irin mummunar barna da ambaliyar ta haddasa a jihohi daban-daban.

Gwamnan Neja Ya Bada Umarnin Rufe Tashar Badeggi FM  Bisa Zargin Tunzura Jama’a

A cewar NEMA, lamarin ambaliyar ya shafi mutum 119,791, yayin da wasu 138 suka samu raunuka daban-daban. Haka kuma, mutum 43,936 sun rasa matsuguninsu, yayin da gidaje 8,594 da filayen noma 8,278 suka lalace ƙurmus.

Rahoton ya kuma nuna cewa ƙananan hukumomi 43 da ke cikin jihohi 19 ne ambaliyar ta fi shafa, inda mata da ƙananan yara suka fi fuskantar tasirin bala’in.

Hukumar ta NEMA ta bukaci haɗin gwiwar hukumomin gwamnati a matakai daban-daban domin ɗaukar matakan gaggawa da na dindindin da za su rage irin wannan ibtila’i a nan gaba.

A cewar hukumar, ya zama dole a ƙarfafa matakan hana gine-gine a hanyoyin ruwa, gina sabbin hanyoyin karkatar da ruwa, da kuma wayar da kan al’umma dangane da yadda za su kare kansu kafin, yayin da kuma bayan aukuwar ambaliya.

Advertisement

 

 

BLUEPRINT

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending