News
Gawuna Ya Jinjinawa Usman Alhaji Kan Tallafa wa Karatun Yara Masu Bukata Ta Musamman
Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano kuma shugaban Babban Bankin Lamuni na Ƙasa (Federal Mortgage Bank of Nigeria), Dr. Nasir Yusuf Gawuna, ya bayyana matuƙar jin daɗinsa da girmamawa ga tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, bisa irin gagarumin taimako da goyon bayan da ya ke bai wa fannin ilimin yara masu buƙata ta musamman.
Dr. Gawuna ya bayyana hakan ne a wajen taron yaye dalibai karo na takwas (8th Speech and Prize Giving Day) na Usman International School da aka gudanar a ranar Lahadi, 3 ga Oktoba, 2025 a Kano, inda ya kasance babban bako kuma shugaban taron.
Najeriya Na Cikin Haɗari Idan APC Ta Sake Lashe Zaɓen 2027 —El-Rufai
Ya ce tsarin ilimi na haɗa yara masu buƙata ta musamman da sauran dalibai da wannan makaranta ta ke aiwatarwa na ɗaya daga cikin manyan ayyuka masu alfanu da ke nuna gaskiyar kishin ci gaban al’umma da jinkai.
“Na shaida abubuwa masu kayatarwa da dama a yau. Na farko, akwai shirye-shiryen bayar da tallafin karatu wanda hakan na nuna alamar kyakkyawar zuciya da kulawa da makomar matasa. Na biyu kuma shi ne tarbiyya da ladabi da nake gani a tsakanin malamai da ɗalibai. Na uku kuma shi ne yadda mai makaranta ke jajirce wajen karɓar yara masu buƙata ta musamman tare da basu dama da kulawa ta musamman don su samu ilimi,” in ji Gawuna.
“Abin ya burge ni ƙwarai. Ina kira ga iyaye da su daina ɓoye yara masu naƙasa a gida. Su turo su makaranta domin su ma su samu damar rayuwa da walwala kamar sauran yara.”
Gawuna ya kuma jinjina wa Alhaji Usman Alhaji bisa sadaukar da rayuwarsa wajen ganin yara da dama sun samu ilimi cikin yanayin da ya dace.
A nasa jawabin, Alhaji Usman Alhaji, wanda shi ne mamallakin makarantar kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, ya bayyana cewa tun lokacin da yake Kwamishinan Ilimi a shekarar 1999 ne ya fahimci muhimmancin gina makarantun zamani da masu hali za su ɗauki nauyin su.
“Na ga dole ne mu masu hali mu taka rawa wajen tallafa wa ilimi, musamman ganin yawan jama’a da ƙalubalen da Arewa ke fuskanta. Wannan makaranta na ta an kafa ta ne da burin ganin yara na kowane matsayi sun samu ilimi da tarbiyya.”
Ya ƙara da cewa makarantar na da ɗalibai kusan 100 da ke amfana da guraben tallafin karatu, inda kusan 30 daga cikinsu ke biyan kaso 50 na kuɗin makaranta.
“Wasu iyaye suna da yara masu hazaka amma ba su da hali. Mu kuma a matsayimmu na ‘yan ƙasa masu kishin kasa, dole mu tallafa musu. Burina shi ne Usman International School ta zamo tamkar makarantar kwarai ta fuskar ilimi, halayya da tarbiyya.”
Shugabar Sashen Buƙata Ta Musamman na makarantar, Malama Hajara Sunusi Hamisu, ta ce suna aiwatar da tantancewar kowane ɗalibi domin gane ƙwarewarsa kafin a shigar da shi cikin tsarin karatu.
“Muna haɗa darussa na boko da sana’o’in hannu. Muna da yara da ke fama da matsalolin gani, ji da ƙwaƙwalwa, amma suna samun ci gaba sosai. Haka kuma, muna da masu taimako da ke kulawa da su a kowace rana.”
Shugaban makarantar, Malam Abdurrahman Ballo Ibrahim, ya bayyana cewa dalibai 40 ne suka kammala karatu a bana, inda ya bayyana Haft Magaji a matsayin ɗalibi mafi hazaka a fannonin Lissafi, Physics, Biology da Civics, yayin da Maryam Sani ta lashe kyaututtuka a Turanci, Biology, Chemistry da Fisheries.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
