News
Jami’in NSCDC Ya Rasa Ransa A Hannun ’Yan Daba A Kasuwar Jigawa
Rundunar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) reshen jihar Jigawa, ta tabbatar da kisan gilla da aka yi wa daya daga cikin kwararrun jami’anta a kasuwar mako da ke Shuwarin, cikin karamar hukumar Kiyawa ta jihar.
Kakakin rundunar, Badaruddin Tijjani, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse ranar Litinin, inda ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:30 na rana, yayin da jami’in ke gudanar da wani aiki na musamman a kasuwar.
Ambaliya Ta Lalata Gidaje, Makarantu Da Gonaki A Bauchi, Filato Da Neja
Marigayin, Bashir Adamu-Jibril, wanda ke rike da mukamin Superintendent of Corps (SC), na sashen leken asiri da bincike ne a rundunar kafin rasuwarsa. An bayyana cewa jami’in ya je wajen kasuwar Kara domin gudanar da aiki na musamman kan wasu da ake zargi da aikata laifuka.
“Bisa bayanan da muka samu, wasu daga cikin masu sana’ar a kara ne suka kai masa mummunan hari da adda, inda suka sare masa bayan kai har lahira,” in ji Tijjani.
A cewar kakakin rundunar, an garzaya da marigayin zuwa Asibitin Gwamnati na Dutse, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Ya kara da cewa rundunar ta kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan, yayin da bincike ke ci gaba domin gano sauran da ke da hannu a wannan ta’asar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
