Connect with us

News

Gidan Rediyo Ya Dakatar Da Babban Darakta Kan Sukar Gwamna

Published

on

images (2)

Gidan rediyo mai zaman kansa a jihar Ebonyi, Legacy FM, ya dakatar da mai rikon mukamin babban darakta, Godfrey Chikwere, bisa zargin yawan yin suka ga Gwamna Francis Nwifuru a shirye-shirye da kuma shafukan sada zumunta.

A wata sanarwa da gidan rediyon ya fitar a ranar Asabar, ya ce matakin ya biyo bayan abin da ya kira “kin bin ka’idojin aiki da rashin ladabi” daga Chikwere.

Gidan Rediyo Ya Dakatar Da Babban Darakta Kan Sukar Gwamna

Sanarwar ta ce: “Hukumar gudanarwar Legacy FM 95.1 na sanar da dakatar da Mista Godfrey Chikwere daga yau zuwa wani lokaci da za a sanar daga baya. Haka kuma an umurce shi da ya mika duk kayan mallakin kamfanin da ke hannunsa ga jami’in da ya fi shi matsayi.”

A rubutun da Chikwere ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, ya zargi gwamnatin Nwifuru da rashin isar da saƙo yadda ya kamata, rashin ingantaccen aiki daga mukarraban gwamnati, da kuma rashin tsare-tsaren da suka fito fili.

Kakakin gwamnan, Monday Uzor, ya ce zarge-zargen Chikwere ba su da tushe, yana masu cewa gwamnati ta yi wa gidan rediyon alheri da dama, amma duk da haka ya maida hankali kan sukar gwamnati.

Ya ce: “Gwamna ya ba gidan rediyo kyautar sabuwar mota kirar Changan SUV, ya ba da sabon injin wutar lantarki, sannan ya gina hanyar da ke kaiwa ofishinsu. Amma maimakon bayar da rahoto mai daidaito, gidan rediyon ya fi mayar da hankali kan sukar gwamnati.”

Advertisement

Shi ma kwamishinan yada labarai na jihar, Ikeuwa Omebeh, ya yi Allah-wadai da kalaman Chikwere, yana masu cewa sun yi tsauri, sun kuma sabawa mutuncin al’ummar jihar.

 

 

 

NIGERIAN TRACKER

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending