Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 13 Yayin Sallar Asuba A Katsina

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Gwamnatin Jihar Katsina ta tura ƙarin jami’an tsaro zuwa ƙaramar hukumar Malumfashi, bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari suka kashe mutane 13 da ke cikin masallaci yayin sallar Asuba a ranar Talata.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr. Nasir Mu’azu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Katsina.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Kara Albashin Masu Rike Da Mukaman Siyasa

A cewarsa, harin na ramuwar gayya ne, sakamakon yadda al’ummar yankin suka taɓa kare kansu daga farmakin ’yan bindiga a baya.

Dr. Mu’azu ya ce an riga an tura jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na jajantawa iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, tare da tabbatar musu da cewa za ta ci gaba da tallafa wa al’umma wajen ƙarfafa yaki da ’yan ta’adda.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending