Connect with us

News

NiMet Ta Yi Hasashen Samun Ruwan Sama Da Iska Na Tsawon Kwana Uku A Najeriya

Published

on

Nimet (1)

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa za a samu ruwan sama mai ɗauke da iska a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Juma’a zuwa Lahadi.

A cewar hukumar, jihohin Arewacin ƙasar da suka haɗa da Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Yobe da Taraba na cikin wuraren da ake sa ran guguwar iska da ruwan sama mai matsakaici.

Advertisement

An Sace Dalibai 330, An Rufe Makarantu 52 A ƙananan hukumomi Uku A Katsina —Rahoto

NiMet ta ce a yankin tsakiyar ƙasa – wato Abuja, Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, Neja da Filato – ana iya samun ruwan sama kaɗan.

Haka kuma, a Kudu, an yi hasashen yanayi mai zafi tare da ruwan sama kaɗan a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ondo, Edo, Enugu, Imo, Abia, Anambra, Delta, Rivers, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.

Advertisement

Hukumar ta gargadi jama’a da su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai yawa, tare da cire na’urorin lantarki daga soket domin kaucewa haɗari. Ta kuma ce ya kamata a guji zama ƙarƙashin manyan itatuwa, da kuma ɗaure kayayyakin da ba su da ƙarfi.

Bugu da ƙari, ta shawarci manoma da su guji amfani da taki da maganin kwari kafin ruwan sama ya sauka, tare da bukatar kamfanonin jiragen sama su riƙa samun rahoton yanayi na musamman kafin su tsara tashi.

Advertisement

 

 

Advertisement

Vanguard

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending