Connect with us

News

Kungiyar Likitocin Sun Saka Lokacin Shiga Yajin Aiki A Najeriya 

Published

on

Kungiyar Likitocin Masu Ƙwarewa a Najeriya (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki goma don ta cika bukatun da likitocin suka dade suna nema, in ba haka ba za su tsunduma yajin aiki a duk faɗin ƙasar nan.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugabancin ƙungiyar ya fitar bayan taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa da suka gudanar ta hanyar taron bidiyo a ranar Lahadi.

Advertisement

Shugaban Ghana Ya Tsige Alkalin Alkalan Kasar

Ƙungiyar ta ce wasu daga cikin bukatun sun haɗa da biyan kuɗin horon likitocin masu neman ƙwarewa na shekarar 2025, da kuma magance jinkirin biyan bashin albashi, musamman ƙarin kaso 25 da 35 a sabon tsarin albashin likitoci. Haka kuma sun nemi biyan kuɗin kayan aiki na shekarar 2024.

Bugu da ƙari, NARD ta bukaci hukumar kula da likitoci da likitocin hakora ta ƙasa (MDCN) ta dawo da amincewa da takardun shaidar ƙwarewar likitoci na Yammacin Afirka. Haka nan ta kuma bukaci cibiyar koyar da manyan likitoci ta Najeriya (NPMCN) da ta gaggauta bayar da takardun shaidar ƙwarewa ga duk wanda ya cancanta ba tare da jinkiri ba.

Advertisement

A matakin jihohi kuwa, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatocin Kaduna da Oyo da su warware matsalolin walwalar likitocin masu neman ƙwarewa a jihohinsu.

Kungiyar ta gargadi gwamnati cewa idan har bukatun ba su samu amsa kafin karewar wa’adin kwanaki goma da suka bayar ba, babu wani zaɓi illa ta tura dukkan mambobinta shiga yajin aiki a duk faɗin ƙasar nan.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending