Connect with us

News

An Kama Wata Mata A Kebbi Bisa Zargin Binne Jaririnta Da Ransa

Published

on

IMG 20250903 WA0052

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kebbi ta kama wata mata mai shekaru 20 da haihuwa, Maryam Atiku, bisa zargin ta yi ƙoƙarin kashe jaririnta ta hanyar binne shi da ransa a ƙauyen Kamba da ke ƙaramar hukumar Dandi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Yuni, 2025, inda ake zargin Maryam ta ɗaure wuyan jaririn da zani, ta rufe bakinsa sannan ta binne shi a cikin wani rami a dajin Malam Yaro.

Advertisement

‎Jihar Kano Ta Saka Ranar Komawa Makarantun Firamare Da Sakandire ‎

A cewar CSP Abubakar, washegari wani manomi mai suna Alhaji Kabiru Muhammad ya gano wurin da aka yi sabuwar rami, ya kira mutane suka tono jaririn, inda aka same shi da rai. An garzaya da shi Asibitin Kamba, inda likitoci suka tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya bayan samun kulawa.

Rundunar ‘yan sanda ta kama Maryam wacce ta amsa laifinta. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bello Sani, ya bayyana cewa wannan lamari abin takaici ne kuma hukumar ba za ta lamunci irin hakan ba.

Advertisement

Kwamishinan ya yaba wa matar gwamnan jihar, Hajiya Zainab Nasir Idris, bisa taimakon da ta bayar ga jaririn da aka ceto, tare da godiya ga Alhaji Kabiru Muhammad da ya gano abin da ya faru cikin lokaci.

An tabbatar da cewa za a gurfanar da Maryam a gaban kotu domin ta fuskanci hukunci bisa laifin da ta aikata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending