Connect with us

News

FRSC Ta Nemi A Bai Wa Jami’anta Ikon Riƙe Bindiga Don Kare Kai

Published

on

FB IMG 1757047534574

Hukumar kula da ababen hawa ta ƙasa (FRSC), Shehu Mohammed, ya ce, jami’an rundunar na son fara riƙe makami saboda yawan haɗuran da ake samu a kan hanya a lokacin da suke bakin aiki.

Mista Muhammed ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da PREMIUM TIMES.

An Kama Wata Mata A Kebbi Bisa Zargin Binne Jaririnta Da Ransa

A halin yanzu akwai doka da ke gaban majalisa da ke neman yin gyara ga hukumar kula da ababen hawa ta ƙasa ta shekarar 2007 domin bai wa jami’an ikon riƙe makami.

Ɗan majalisar Abiodun Adesida (APC, Ondo) da Olaide Muhammad (APC, Oyo) ne suka gabatar da ƙudurin kuma har ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.

Sai dai masu sukar wannan ƙuduri na bai wa FRSC damar riƙe makami na ganin cewa hukumar za ta iya haɗa kai da wasu jami’an tsaro da ke da izinin ɗaukar bindiga kamar ‘yan sanda domin gudanar da ofureshan na musamman.

Sai dai mista Muhammed ya tsaya kai da fata kan wannan buƙata.

Advertisement

Ya kuma yi ƙarin haske kan cewa buƙatar riƙe makamin ya zama wajibi saboda rundunar ta rasa jami’anta sama da 200 tun bayan kafa sakamakon masu ababen hawa da ke yin tafiyar ruwa da su. Ya ƙara da cewa kuma babu wani daga cikin waɗannan matuƙa ababen hawa da suka iya kamawa.

Ya kuma ce rundunar na son bai wa jami’anta makamai ne domin kare rayuwarsu a yayin da suke aiki a kan tituna a faɗin ƙasar nan.

“A shekarar da ta wuce, ina tunanin akwai jami’anmu kusan 200 – jami’ai waɗanda aka buge, kuma adadin ya kai sama da 240 tun bayan kafa hukumar. A yayin irin wannan ibtila’in, waɗanda suka aikata laifin sukan tsere ne,” ya faɗa.

A yayin da yake magana game da fargabar da al’umma ke yi kan bai wa jami’an FRSC makami, Mista Mohammed ya ce, ba dukkan jami’an za a bai wa makami ba idan har majalisa ta amince da gyaran dokar.

Ya kuma ce waɗanda za a ba wa makamai za su amfani da su ne kawai idan sun samu kiran mai cike da fargaba daga sauran jami’ansu.

Ya ce, rundunar na shirya wa irin wannan tsarin aiki ta hanyar tabbatar da an horas da waɗanda za a bai wa makamai.

Advertisement

“Wani rukuni ne, tawaga ta waɗanda suka samu horaswa, da za su iya riƙe makamai domin kai ɗauki za a amince su ɗauki makami.”

“Haka kuma, idan za ka iya tunawa, wasu shekaru da suka wuce, muna da makamai. Muna yin horaswa, kuma mafi yawansu sukan samu horaswa ne a Jaji. Na yi nawa ne a Keffi. Wasu kuma sun yi nasu a jihar Legas, wasu a Jos da Enugu. A wancan lokaci an ma sayo makaman ne inda muka gina wurin ajiye makamanmu a Gwagwalada. Mun kuma haɗaka kai da wani Kanal na soja (mai ritaya).

Sannan Muhammed ya ce, “Me jami’in FRSC zai yi idan ya tare mota kamar tanka ko tirela musamman masu yin lodin abubuwa daban-daban? Za ka ga mota da dabbobi da kuma fasinjoji 100. Ta yaya za ka tsayar da su idan jami’in ba shi da makami? Don haka, akwai buƙatar juyawa ka kare kansa.”

“Ba kowa za ka ba wa makami ba ya hau kan hanya ba. Wannan ne ya sa mutane suke fargaba kan bai wa jami’an FRSC makami. Mu ma za mu kula. Wanna ne ya sa ba kowa ne zai riƙe abin kare kai ba.”

Gama da matsayar dokar:

Game da matsayar dokar a zauren majalisa kuwa, mista Mohammed ya ce, an majalisar wakilai ta amince da ƙudurin. Tana jiran takwararta ta Dattajai ne su duba ƙudurin.

Advertisement

“Akwai ƙudurin dokar a gaban majalisa, sai dai bayan zuwan tsohon shugaban ƙasa Mohammadu Buhari, shi ne ba cigaba da duba dokar ba. Amma a wannan lokaci, muna ƙoƙrin ganin ta tabbata, mun kafa runduna ta musamman.”

Sannan ya ce suna so a sake duba hukuncin wasu laifuka da ba a mutunta su saboda akwai wasu da suke biyan kuɗin tara su ce a ajiye idan sun aikata irin laifin a gaba shikenan. Ya ce, wannan na faruwa ne saboda tarar ba ta da yawa.

Game da walwalar jami’an hukumar:

Muhammed ya jaddada cewa, akwai buƙatar a inganta walwalar jami’an hukumar domin ƙara musu karfin guiwa da daidaito wajen gudanar da ayyukansu.

“Muna son a duba walwala. Wani abu ne da ma’aikatanmu ke son a duba musu. Kuma a cikin batun walwalar nan akwai batun idan jami’i ya gama aiki a matsayin mataimakin marshal (ACM), ko mataimakin ‘corps marshal’ (DCM), a cigaba da biyasa albashisa yadda yake har ƙarshen rayuwarsa kamar yadda manyan jami’an ‘yan sanda kamar DIGs, AIGs. Yanzu an faɗaɗa wannan zuwa ga jami’an kare kadarorin gwamnati da al’umma (civil defence) da jami’an hukumar shigi da fice. Muna bai kamata a ware mu ba,” ya faɗa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending