Connect with us

News

Yan Ta’adda Da Dama Sun Mutu Yayin Wani Harin Sojojin Saman Najeriya

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da halaka sama da ‘yan ta’adda 15, a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame, ya tabbatar da haka a wata sanaarwa da ya fitar a safiyar wannan alhamis.

Advertisement

FRSC Ta Nemi A Bai Wa Jami’anta Ikon Riƙe Bindiga Don Kare Kai

Ehimen Ejodame, yace wannan gagarumar nasara da rundunar samu, na zuwa ne bayan wasu hare-haren jirage da suka kai, a maɓoyar ‘yan ta’addan ranar Laraba, tare da lalata muhimman gine-ginen su a Zuba, da ke jihar Borno.

A cewarsa, tun a ranar 3 ga watan da muke ciki na Satumba ne, rundunar sojin Najeriya, ta tsara yadda ya kamata akai harin zuwa sabon yankin da ke fama da ayyukan ta’addanci a yammacin Zuwa da ke Sambisa

Advertisement

Ya ƙara da cewa, farmakin na baya-bayan nan ya ƙara dakushe ƙarfin ‘yan ta’adda a yankin, sannan ya nuna yadda rundunar sojin saman Najeriya ke ƙoƙari a yaƙi da ta ke yi da ta’addanci a faɗin ƙasar.

Ehimen, ya kuma jaddada yadda irin jajircewa da dakaarun sojojin sama ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, yayin da suke tallafawa sojojin ƙasa a ayyukan haɗin gwiwa don murƙushe ayyukan ta’addanci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending