Connect with us

News

El-Rufai Ba Shi Ne Mai Gidana Ba  —Gwamna Uba Sani

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya musanta zargin cewa yana ƙarƙashin tasirin tsohon gwamna Malam Nasir El-Rufai, inda ya ce siyasar da yake yi ta samo asali ne daga shugabanni daban.

A cikin wata tattaunawa da gidan talabijin na TVC, gwamnan ya ce shugabannin da suka fi yi masa jagora tun farko sun haɗa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da marigayi lauya mai kare haƙƙin ɗan adam, Cif Gani Fawehinmi.

Advertisement

’Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Mutum 7, Sun Jikkata 11 A Sabon Hari A Kaduna

Gwamna Uba Sani ya ce ba ya son tsayawa yin musayar kalamai kan batutuwan jagoranci, domin a cewarsa, babban burinsa shi ne samar da mulki nagari ga al’ummar Kaduna.

Ya kuma karyata rade-radin cewa gwamnatinsa tana biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga, yana mai cewa, “Ba mu taɓa biyan ko sisi ga wani ɗan bindiga ba. Wadanda ke yada wannan magana siyasa kawai suke yi.”

Advertisement

Game da batun tsaro, gwamnan ya ce gwamnatinsa na aiki da dabarun soji tare da tattaunawa da shugabannin al’umma musamman a yankin Birnin Gwari, inda ya ce tsarin haɗin kai ya fara kawo sauyi.

Dangane da rikicin da ya faru a wani taron jam’iyyar adawa a Kaduna kwanan nan, Gwamna Uba Sani ya nesanta kansa daga lamarin, yana mai cewa shi wanda aka taɓa tsare sau biyar saboda fafutukar kare dimokuraɗiyya, ba zai goyi bayan wani abu da zai tauye ’yancin jama’a ba.

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending