News
Majalisa Ta Hana Sanata Natasha Komawa Aiki Duk Da Cikar Watanni 6 Na Dakatarwa
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ce Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba za ta iya komawa bakin aiki ba duk da cewa wa’adin dakatarwar da aka yi mata ya cika.
Sanatar Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa majalisar wasika inda ta sanar da ita cewa watanni shida sun cika, don haka za ta koma majalisar dattawa.
Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Kusa Fara Cin Bashi Daga Opay Da Moniepoint —Dino Melaye
Sai dai mai rikon sakataren majalisar, Yahaya Danzaria, ya bayyana cewa batun dakatarwar har yanzu yana gaban kotu.
“Batun dakatarwarki na gaban Kotun Daukaka Kara a halin yanzu. Saboda haka sai an kammala shari’ar sannan majalisar dattawa ta sake duba batun bisa hukuncin kotu,” in ji Danzaria a cikin wasikar da AIT ta gani.
A baya, a ranar 12 ga Yuli, Natasha ta yi ƙoƙarin komawa bakin aiki bayan Babbar Kotun Tarayya ta umurci majalisar dattawa da ta sake duba dakatarwar. Amma jami’an tsaro suka hana ta shiga harabar majalisar.
Tun daga lokacin, bangarorin biyu – wato Natasha da majalisar – sun ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Daukaka Kara, inda ake jiran ci gaba da sauraron shari’ar.
