News
Cutar Mashako Tayi Ajalin yara 10 A Neja
Akalla yara goma sun mutu a sakamakon barkewar cutar Mashako a ƙananan hukumomin Agaie da Bida da ke Jihar Neja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yaran da abin ya shafa an kai su Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Bida (FMC Bida), inda daga baya suka mutu.
Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum Daya, Ta Yi Awon Gaba Da Uwa Da Ɗanta A Zariya
Haka kuma, an ruwaito karin mace-mace a wasu yankuna da ke cikin ƙananan hukumomin biyu tun bayan bullar cutar.
Wani mazaunin garin Bida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce al’ummar yankin na cikin tsananin fargaba kan yadda cutar ke ci gaba da ƙara yaduwa.
“Wannan lamari na rayuwa da mutuwa ne. Muna kira ga gwamnatin jiha ta samar da magunguna cikin gaggawa a asibitocin Agaie da Bida domin dakile yaduwar cutar zuwa sauran wurare,” in ji shi.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiyar Manyan Asibitoci ta Jihar Neja, Dr. Mohammed Gana, ya tabbatar da bullar cutar lokacin da DAILY TRUST da ta tuntube shi.
Ya ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomin kiwon lafiya na ƙasa sun fara daukar matakan gaggawa don dakile cutar tare da samar da magunguna ga asibitoci.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
