News
Shettima Ya Yabawa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Kwarewa Ta Jihar Kaduna
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa kafa Majalisar Kwarewa ta farko a matakin jiha a Nijeriya, yana mai bayyana wannan mataki a matsayin ci gaban da ya dace sauran jihohi su yi koyi da shi.
Shettima ya yi wannan yabo ne a yayin taron karo na bakwai na Majalisar Ƙasa kan Kwarewa (NCS), wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata.
INEC Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC
Ya bayyana cewa juyin juya halin kwarewa shi ne ginshiƙin yarjejeniyar gwamnatin Tinubu da ‘yan Nijeriya, kana muhimmin mataki ne wajen cika alƙawarin bunƙasa jari-hujjar ɗan adam.
Mataimakin Shugaban Ƙasan ya jaddada cewa shigar sama da dalibai 30,000 cikin Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa ta Kaduna, na nuna tsayin dakan gwamnatin jihar wajen samar da ayyukan yi da bunkasa kwarewar matasa.
Haka kuma, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa, ya jinjinawa rawar da Gwamna Uba Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da cibiyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana ci gaba da sake fasalin makarantun fasaha a fadin ƙasar domin mai da hankali kan darussa masu amfani da tasiri.
Shettima ya kuma bukaci mambobin Majalisar Kasa kan Kwarewa da su yi aiki tare wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su tabbatar da juyin-juya halin tattalin arzikin Nijeriya. A cewarsa, “ba za mu iya gina ma’aikata da za su iya tsayawa a gaban ƙalubale na gaba ba kan tushen rarrabawa.”
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
