Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Za A Samu Ambaliya A Wurare 32, Ciki Har Da Kano

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wurare 32 da ke cikin jihohi 11, ciki har da Jihar Kano, daga ranar 14 zuwa 18 ga Satumba, 2025. Hasashen na zuwa ne sakamakon ruwan sama mai tsanani da ake sa ran zai ratsa sassan ƙasar nan a makon nan.

 

Advertisement

Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa ce (National Flood Early Warning Systems Centre) ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli wacce  Darakta cibiyar Usman Abdullahi Bokani ya rattaba wa hannu, inda ta bukaci hukumomi da al’umma su ɗauki matakan kariya.

Jami’an NDLEA Sun Kama Ɗan Indiya Da Wasu ’Yan Najeriya 3 Da Tramadol Ta N3.9bn A Filin Jirgin Sama

‎Jihohin da ke cikin haɗari sun haɗa da Adamawa, Benue, Nasarawa, Taraba, Delta da Neja, tare da wasu yankuna a Kebbi, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara. A cewar sanarwar, karin ruwa a kogunan Gongola, Benue da Neja ya ƙara tayar da barazana, inda aka shawarci al’ummomin da ke bakin koguna da su gaggauta barin wuraren kafin lamarin ya tsananta.

Advertisement

‎Gwamnatin ta kuma yi kira ga hukumomin jihohi, cibiyoyin bada agajin gaggawa da shugabannin al’umma da su ɗauki matakai cikin gaggawa domin rage yiwuwar asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliyar ka iya haifarwa. jawo.

 

Advertisement

 

KANO TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending