Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Ɗan Indiya Da Wasu ’Yan Najeriya 3 Da Tramadol Ta N3.9bn A Filin Jirgin Sama

Published

on

WhatsApp Image 2025 09 14 at 11.32.18 2

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta cafke wani ɗan kasuwa ɗan Indiya, Gupta Ravi Kumar, tare da wasu ’yan Najeriya uku bisa zargin shigo da tramadol guda miliyan 2.2 da darajarsu ta kai Naira biliyan 3.9, ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA), Ikeja, Legas. An ce ƙwayoyin an shigo da su daga Delhi, Indiya, a cikin kwalaye 114 da aka boye a matsayin magungunan multivitamins, ta jirgin Ethiopian Airline

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya ce jami’an NDLEA sun sa ido kan kayayyakin har tsawon kwanaki, kafin daga bisani su cafke wasu direbobi da wakilin kwastan da ke ƙoƙarin fitar da su. Sai dai a safiyar Juma’a, jami’an hukumar suka cafke ɗan kasuwar Indiya, Gupta Ravi Kumar, bayan da ya bayyana domin karɓar kayan da aka ɓoye, abin da ya tabbatar da rawar da yake takawa a safarar.

Advertisement

Ƙungiyar Likitoci Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gargadi Da Ta Shiga

A wani samame daban a Legas, jami’an NDLEA sun cafke wani fasinja da ya nufi Doha da jirgin Qatar Airline da gram 900 na wiwi da aka boye cikin kifaye, wanda ya kai ga cafke wani abokin harkallarsa a otal da ke Ajao Estate. Haka kuma an gano kilo 81.7 na wiwi da 1.2kg na hashish oil daga wani kwantena da aka shigo da shi daga Canada, tare da cafke mutane biyu, da kuma ƙarin kilo 65 na wiwi daga wata mota kirar Toyota Sienna a gadar Third Mainland.

Bugu da ƙari, hukumar ta gano wani masana’anta a Ikorodu da ke kera abin sha mai haɗa wiwi da ake kira skuchies. An kwace kwalabe 6,029 na wannan giya da kuma kilo 4,232 na wiwi, tare da kama mutane biyu da ake zargi. A wasu jihohin Najeriya kuma, an yi nasarar cafke mutane da dama da kwayoyi, ciki har da Abuja, Kano, Anambra, Yobe, Ogun da Edo, inda aka kwace daruruwan kilo na miyagun ƙwayoyi da gonakin wiwi.

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending