Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Makaniken Da Ya Sace Motar Abokiyar Cinikiyyarsa A Kano

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan sanda a Jihar Kano ta kama wani makanike mai shekaru 42 daga unguwar Sharada bisa zargin guduwa da motar wata kwastoma kirar Mercedes-Benz da aka kai masa domin gyara.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Za A Samu Ambaliya A Wurare 32, Ciki Har Da Kano

Ya ce matar da ta kai motar domin a gyara na’urar sanyaya iska (A/C) ta mika ta ranar 28 ga watan Agusta, 2025, amma makaniken ya yi gaba da ita. Wannan ne ya sa Kwamishinan ’Yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bada umarnin gaggawa ga tawagar bincike bisa jagorancin Sufeto-Janar na ’Yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun.

Binciken ya gano cewa wanda ake zargin ya tsere zuwa Kaduna, inda ya sayar da motar Mercedes-Benz ɗin, ya karɓi wata mota kirar Toyota Corolla da kuma ƙarin naira miliyan bakwai a matsayin canji. Rundunar ta ce an kama shi tare da kwato Toyota Corolla ɗin, yayin da ake ci gaba da neman motar Mercedes-Benz.

Advertisement

Kwamishinan ’Yan sanda ya godewa jama’a bisa haɗin kai, tare da tabbatar musu cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, sannan kuma duk masu aikata laifi za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending