Connect with us

News

An Kama Wata Mata Bisa Zargin Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 

Published

on

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da cafke wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar.

A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Satumba, 2025, bayan wata sa-in-sa da ta barke tsakanin ’yan uwan biyu kan bashin N800.

Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Kauyuka 13 A Adamawa

Ayanlade ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta, lamarin da ya sa ta faɗi ƙasa, daga bisani ta rasu.

Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je gidan yayarta, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karɓar bashin N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai rigimar da ta fara a matsayin ƙaramin sabani ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta ture marigayiyar har ta fāɗi ƙasa.”

“Abin takaici, duk da cewa an garzaya da marigayiyar asibiti don kulawar gaggawa, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba,” in ji shi.

Rundunar ta tabbatar da cewa an kama wadda ake zargi kuma tana tsare da ita a halin yanzu, yayin da bincike ke ci gaba.

Advertisement

A cewar sanarwar, za a gurfanar da Bosede a gaban kotu bayan kammala bincike, domin ta fuskanci hukunci kan abin da ya aikata.

TRUST RADIO 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending