Connect with us

News

Wani Mai Tsaurin Ido Ya Sace Munduwar Fir’auna A Gidan Tarihin Masar

Published

on

Untitled design 26

Hukumomin Masar sun kaddamar da gagarumin samame a sassan ƙasar bayan wani mai tsaurin-ido ya sace munduwar zinari ta Fir’auna mai shekaru dubu 3 da aka adana a gidan tarihin birnin Alkahira.

Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi batan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita.

Advertisement

Abba Anwar Ya Kalubalanci Ganduje Kan Rashin Tabuka Abun A Zo A Gani A Bangaren ilimi A Kano Ta Arewa

An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta zuwa ƙetare.

Munduwar mai ɗauke da ado na musamman, na da matuƙar daraja tun zamanin Fir’aunan, yayin da ake danganta ta da tsoffin gumakan da aka yi bautar su a can baya, sannan an ce tana da ƙarfin warkarwa.

Advertisement

Munduwar na cikin jerin kayayyakin tarihin da ake shirin zuwa da su wani gagarumin taron baje-kolin kayayyakin tarihi a Italiya da za a fara gudanarwa a watan gobe.

Tuni aka kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan sauran kayayyakin tarihin da ake da su a ƙasar domin tabbatar da cewa, suna nan daram.

Advertisement

Gidan tarihi na Masar shi ne mafi daɗewa a yanƙin Gabas ta Tsakiya, kuma yana ɗauke da kayayyaki daban-daban har guda dubu 170.

 

Advertisement

 

FRI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending