Connect with us

News

Kungiyoyin Arewa 45 sun gamsu Shugaban kasa ya fito daga Kudu a zaben 2023.

Published

on

Daga mujahid danlami garba

 

 

Gamayyar kungiyoyi masu cin gashin kansu 45 daga jihohin Arewacin Najeriya da Abuja sun nuna rashin goyon bayan yankin ya cigaba da mulki.

Jaridar Punch ta ce wadannan kungiyoyin su na goyon bayan mulki ya koma kudancin kasar nan.

‘Yan tafiyar Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria sun bayyana cewa za su yi adawa ga duk ‘dan takarar da aka tsaida daga Arewa.

Advertisement

A cewar Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria, idan za ayi adalci da zaman lafiya, daga kudu ya dace a samu magajin Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun bakin kungiyar, Abdulsalam Mohammed-Kazeem ya fitar da jawabin matsayar da suka cin ma a wajen taron manema labarai.

Ganin zabe ya karaso, Abdulsalam Mohammed-Kazeem sun yi wannan taro ne a dakin Arewa House da ke Kaduna kamar yadda aka kawo rahoto a jiya.

A cewar sa, ‘yan Arewa sun yi shekara da shekaru su na rike da Najeriya, amma hakan bai iya magance talauci da rashin tsaro ba.

A taron da aka yi ranar Laraba, gamayyar kungiyoyin ta gargadi jam’iyyun siyasa da cewa ka da su ba wani mutumin Arewa tikitin takarar shugaban kasa.

Shugaban ya yi kira ga jam’iyyu su ware tutar 2023 ga ‘yan Kudu domin a kara dankon zumuncin da ke tsakanin mutanen yankin da takwarorinsu na Arewa.

Advertisement

Duk da bai cikin doka, Kazeem ya ce zai yi kyau a ba sauran bangarori damar yin mulki domin hakan zai inganta kaunar juna da ‘yanuwantaka a Najeriya.

Abin da wannan kungiya ta ke so shi ne mutumin Ibo ya zama shugaban kasa tun da yankin kudu maso yamma sun ci moriyar tikitin APC tun 2015.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending