News
Gwamnatin Kano Ta Bayyana Nasarorin Da Aka Samu A Bangaren Tsaro Da Farfado Da Rayuwar Matasa A Bikin Cikar Najeriya Shekaru 65
Gwamnatin Jihar Kano ta yi amfani da bikin cikar Najeriya shekaru 65 wajen bayyana nasarorin da aka samu a bangaren tsaro da farfado da rayuwar matasa a cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce shirin Safe Corridor Initiative – The Kano Model ya taimaka wajen rage tashin hankali da laifuka da matasa ke yi. Shirin yana aiki tare da ‘yan sanda da hukumar NDLEA, yana wayar da kan matasa da horar da su kan sana’o’i domin su koma cikin al’umma cikin mutunci.
Ƴan Sanda A Indiya Sun Cafke Ɗan Najeriya Da Ya Damfari Mata Sama Da 100
Waiya ya ce shirin ya mayar da hankali kan matasa masu tuba daga aikata laifuka, rigingimun siyasa, da wadanda ke shaye-shaye ko suka daina karatu. A shekarar 2024 kadai, hukumar NDLEA ta kama 1,345 mutane, ciki har da 1,301 maza da 44 mata.
A madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Shugaban Ma’aikatan sa, Dakta Suleiman Wali Sani, ya jaddada cewa gwamnatin za ta ci gaba da baiwa ilimi muhimmanci wajen farfado da matasa da karfafa su su dogara da kansu. Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su karɓi katin zaɓe (PVC) domin su taka rawar gani a zabe mai zuwa.
Taron ya samu halartar wakilan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, jami’an hukumar zaɓe, kungiyoyin farar hula, jami’an gwamnati, dalibai da ‘yan jarida.
