News
Kotu Ta Daure Mutumin Da Ya Yanka Talotalo Ya Sha Romonsa
Kotun Florida a Amurka ta aike da wani mutum gidan wakafi sakamakon zargin yanka tsuntsayen Dawisu tare da yin dabge da naman.
Hukumomin Hudson na Florida suncafke mutumin mai shekaru 61 bayan samun rahoton aika-aikar da ya yi na kashe Dawisu.
Magajin Gari Ya Sasanta mazaunan Paris Da Beraye Don Su Zauna Lafiya
Mutumin dai ya amsa laifinsa na yanka Dawisun guda biyu biyo bayan bacin ran da ya samu da makwabciyarsa wacce ke ciyar da tsuntsayen yayinda shi kuma ya sanar da ita cewa sam baya bukatar ta rinka ciyar da su.
Tuni kotun Florida ta aike da mutumin gidan wakafi. Kotun dai ba ta kai ga tabbatar da makomar sauran tsuntsayen ba, kasancewar mutumin ya sha alwashin kashe su duka da zarar ya fito daga gidan yari idan har makwabtansa basu daina ciyar da su ba
