News
Magajin Gari Ya Sasanta mazaunan Paris Da Beraye Don Su Zauna Lafiya
Birnin Paris, wanda ke ɗaya daga cikin manyan biranen duniya masu fama da yawaitar beraye, An ga wani sabon salo na zaman lafiya tsakanin mutane da waɗannan ƙananan dabbobi wato beraye.
Magajin gari, Grégory Moreau, ya kaddamar da gangamin wayar da kai na musamman don sasanta mazauna birnin da beraye, a cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa bangarorin biyu za su zauna cikin mutunci da haɗin kai.
Magajin Gari Ya Sasanta mazaunan Paris Da Beraye Don Su Zauna Lafiya
A cikin wannan shirin, Moreau ya jaddada muhimmancin bera a cikin rayuwar birni, yana mai cewa, “Rayuwa da beraye na da matukar amfani; ba sa haifar da illa ga mutane idan aka kula da su yadda ya kamata. Su ma suna jin daɗin yadda ake yi musu hidima.”
Gangamin ya haɗa da wayar da kan jama’a game da mahimmancin kiyaye tsaftar muhalli, samar da wuraren da suka dace da beraye, da kuma rage tashin hankali da rikice-rikicen da ake samu tsakanin mutane da dabbobin.
Wannan sabon tsari na Moreau yana nuna yadda birnin Paris ke neman warware matsalolin beraye ta hanya mai tausayi da ilmantarwa, maimakon amfani da hanyoyin tashin hankali ko kashe su.
