Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Sace Hakimi A Kano

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen sace Hakimin Garin Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari, a shekarar 2023.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Advertisement

Dabarun Soji Sun Halaka Gwamman ‘Yanta’adda Tare Da Kame Ɓatagari 450

 

Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Usman Lawan Baba, wanda aka fi sani da “Yellow,” mai shekara 27, a ranar 2 ga watan Oktoba, 2025, a garin Dakatsalle da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji.

Advertisement

Wanda ake zargin tare da wasu sun sace hakimin sannan suka ƙwace masa kuɗi har Naira miliyan 2.75, waya ƙirar Tecno Kevo 4 da kuma agogo.

Daga baya ’yan sanda sun ceto hakimin bayan sun fatattaki ’yan bindigar.

Advertisement

Yayin gudanar da bincike, Baba, ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka aikata laifin, inda ya bayyana cewa Naira 6,000 aka ba shi a matsayin rabonsa.

Ya kuma bayyana sunayen wasu daga cikin abokan aikinsa.

Advertisement

Wasu daga cikinsu sun muty a hannun jami’an tsaro a yayin wasu samame da aka kai, kamar su Bello Kici-Kici daga Doguwa da Mallam Sale daga Gezawa.

Wani kuma mai suna Ruwa Shehu daga Bebeji, yana gidan yari bayan samun sa da laifin satar mutane.

Advertisement

Sauran da suka haɗa da Ibrahim Gwanja da Sule Naye har yanzu ana ƙoƙarin gano inda suka shiga.

’Yan sanda sun ce za a gurfanar da Baba a kotu bayan an kammala bincike.

Advertisement

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa rundunar da ke yaƙi da garkuwa da mutane, bisa jajircewarsu, tare da gode wa jama’a kan goyon bayan suke bai wa jami’an tsaro.

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending