Connect with us

News

Kananan Hukumomi 751 Cikin 774 A Najeriya Na Fama Da Matsalolin Rashin Gaskiya Da Cin Hanci Da Rashawa — Rahoto

Published

on

751 LGAs lagging behind in fiscal transparency accountability – Report 1536x816

Wani sabon rahoto da Cibiyar Binciken Gaskiya da Tsabtace Harkokin Kudi (CFTPI) ta wallafa ya gano cewa mafi yawan kananan hukumomi a Najeriya na fama da matsalolin rashin gaskiya, boye bayanai, da kuma hadarin cin hanci da rashawa.

Rahoton mai taken “Nigerian Local Government Integrity Index (NLGII)” ya nuna cewa daga cikin kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin kasar, 751 — wato kashi 85 cikin 100 — suna cikin rukuni mai “hadari sosai” ko “mai matuƙar hadari.” Rahoton ya danganta wannan mummunan matsayi da rashin bude bayanan kudi ga jama’a da kuma raunin aiwatar da dokokin da suka shafi gaskiya da kulawa da kudaden jama’a.

Advertisement

‎Akalla Mutane Hudu Ne Suka Rasu Bayan Da Hilux Ta Yi Karo Da Tankar Gas A Kaduna

Cikin kananan hukumomin da aka sanya cikin rukuni mafi hadari sun haɗa da Port Harcourt, Southern Ijaw, Ohaji/Egbema da Magu, yayin da kaɗan daga cikinsu kamar Nasarawa (Nasarawa LGA), Dutse, Ikeja da AMAC (FCT) suka samu matsayin “mai kyau” bisa tsari da gudanarwa.

Shugaban CFTPI, Dr. Umar Yakubu, ya ce wannan shi ne rahoto na farko da ya gudanar da cikakken tantancewa kan gaskiya da hadarin cin hanci a matakin kananan hukumomi a Najeriya. Ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci irin su EFCC da ICPC da su maida hankali kan kananan hukumomin da ke cikin rukuni mafi hadari domin dakile wannan matsala da wuri.

Advertisement

Shi ma shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu (SAN), ya yaba da rahoton, inda ya ce za su yi nazari kan sakamakon tare da amfani da shi wajen ƙarfafa shirin hukumar na Accountability and Corruption Prevention in Local Governments (ACCP-LG) domin ganin an inganta gaskiya da rage cin hanci a matakin ƙananan hukumomi.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending