News
Jami’an Tsaro Sun Kama Mutane Biyu da Suke Kai wa ‘Yan Bindiga Kayan Masarufi
Jami’an sa-kai na tsaro a jihar Kogi sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindigar daji kayan masarufi da sauran taimako a yankin Itedo-Ijowa, Isanlu, karamar hukumar Yagba East ta jihar.
Wadanda aka kama sun hadar da Abayo David da David Bori, dukkansu mazauna Itedo-Ijowa. An kama su ne da misalin karfe 4:00 na asuba a ranar Laraba yayi sintirin da jami’an tsaro ke gudanarwa domin tabbatar da tsaro a yankin.
Wasu Fusatattun Matasa Sun Kone Mutum 3 Kurmus Bisa Zargin Garkuwa
Mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Yagba West, Adeyemi Babarinde Sunday, ne ya tabbatar da kama mutanen a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
A cewar Babarinde, wannan kama na daga cikin matakan da hukumomi ke dauka domin dakile wadanda ke taimaka wa masu aikata laifuka da ke barazana ga tsaron al’umma.
“Kama wadannan mutane babban ci gaba ne a yaki da masu bai wa ‘yan ta’adda tallafi da bayanan sirri. Muna da cikakken niyyar samar da zaman lafiya a al’ummominmu, kuma za mu dauki mataki mai tsauri kan duk wanda ke taimaka wa masu tada kayar baya,” in ji shi.
Rahotanni sun ce bayan kama wadanda ake zargin, an kira iyayensu zuwa fadar Aro na Itedo-Ijowa domin yi musu tambayoyi a gaban majalisar gargajiya.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun ce bincike yana ci gaba domin gano ko akwai wasu da ke da alaka da su ko da wata babbar kungiyar ‘yan ta’adda.
