News
Jihar Kano Ta Jaddada Kudirin Cigaba da Samar da ingantattun ayyukan lafiya Ga Jama’ar Jihar
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da kudirinta na ci gaba da samar da ingantattun ayyukan lafiya ga jama’ar jihar, yayin da ta gudanar da taron manema labarai domin tunawa akan Ranar Kula da Lafiyar Ido ta Duniya (World Sight Day), da Ranar Lafiyar Hankali ta Duniya (World Mental Health Day), da kuma Makon Gwajin Cututtukan Tarin Fuka ga Yara (National Childhood TB Testing Week).
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Abubakar Labaran Yusuf, shi ne ya jagoranci taron, inda ya bayyana cewa wannan hadadden taron ya nuna irin jajircewar Gwamnatin Jihar Kano, wajen tabbatar da cewa lafiyar al’umma tana daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci.
Dokta Abubakar ya bayyana cewa manufar taron ita ce wayar da kan al’umma game da manyan matsalolin lafiya da ke addabar jama’a, musamman cututtukan ido, matsalolin tabin hankali, da kuma tarin fuka a cikin yara.
Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa mata ne suka fi kamuwa da matsalolin lafiyar hankali, don haka akwai bukatar a kara azama wajen fadakar da jama’a.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da kiyaye tsaftar jiki da muhalli, tare da hanzarta kai rahoton duk wata alamar rashin lafiya zuwa cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa.
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News18 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
