News
An Kama Wata Mata Bisa Zargin Kashe ’Ya’yanta Biyu
Wata mata mai shekaru 43 ta shiga hannun ’yan sanda a ƙasar Ingila bisa zargin kashe ’ya’yanta guda biyu a cikin gidansu da ke kan titin Corporation Street a garin Stafford.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Asabar da misalin ƙarfe 7:30 na safe, bayan da ma’aikatan asibiti suka kira ’yan sanda don neman taimako. Da isar su wurin, sai suka tarar da yaran biyu sun mutu.
Shugabannin Kafofin Yada Labarai A Kano Sun Bukaci Jama’a Su Yi Rijistar Katin Zabe
Rundunar ’yan sandan Staffordshire ta tabbatar da cewa an kama matar bisa zargin kisan kai, kuma tana tsare a hannunsu domin ci gaba da bincike.
Har yanzu ba a bayyana shekarun yaran ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin mutuwar su.
Jami’ar dake kula da binciken, Det. Insp. Kirsty Oldfield, ta yi kira ga jama’a da su guji yada jita-jita ko yin zato, domin hakan na iya kawo cikas ga bincike da kuma ƙara raɗaɗi ga iyalan yaran.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
