News
Sojan Najeriya Ya Kashe Kansa Bayan Ya Halaka Matarsa
Wani sojan Najeriya mai suna Akenleye Femi da ke aiki a bataliya ta 221 a barikin Wawa da ke karamar hukumar Borgu a jihar Nija ya halaka kansa bayan ya kashe mai dakinsa.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025, inda ya jefa mazauna barikin cikin tashin hankali da mamaki kan abin da ya iya haifar da hakan.
Mai rikon mukamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soji ta 22, kaftin Stephen Nwankwo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa marigayin yana aiki a bataliya ta 221 da ke barikin Wawa kafin rasuwarsa.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa wannan mummunan lamari.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
