News
‘Sai Mun Yi Tafiyar Sama Da Kilomita Biyu Kafin Mu Sami Ruwa’ — Cewar Mazauna Kunshe A Minjibir
Al’ummar Kunshe a Gwado, da ke cikin mazabar Gandurwawa a karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano, sun bayyana damuwa kan rashin ababen more rayuwa da suka haɗa da ruwan sha, hanya, asibiti, da makarantar Boko da ta Islamiyya.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa suna fuskantar matsanancin ƙarancin ruwa, inda suke yin tafiya mai nisa — sama da kilomita biyu — kafin su samu ruwan sha ko na sauran bukatun yau da kullum.
Majalisar Masarautar Kano Ta Taya Maude Murnar Samun Mukamin SAN Da Nadin Kwamishinan Shari’a
“Kullum da safe sai mu tashi mu nufi rijiyar da take da nesa sosai kafin rana ta yi zafi. Idan rijiyar ta bushe, sai mu nufi wani gari da ke da nisa sosai domin samo ruwa,” in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.
Mazauna yankin sun kuma ce mata masu juna biyu na fuskantar ƙalubale wajen zuwa asibiti, musamman a lokacin haihuwa ko rashin lafiya, abin da ke jefa su cikin haɗarin rasa rayuwa.
Wasu daga cikin matasan garin da iyaye mata sun nuna damuwa kan halin da suke ciki, inda suka roƙi gwamnatin jihar Kano da ta karamar hukumar Minjibir su gaggauta kawo musu ɗauki, musamman wajen samar da ruwan sha da gyaran hanyoyi.
Da Jaridar Kadaura24 ta nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar Minjibir, Hon. Captain Jibrin Nalado, ta wayar salula bai daga ba. Sai dai daga bisani ya amsa ta saƙon rubutu inda ya ce:
“In sha Allah muna ƙoƙari a duk garuruwan da ke fama da irin wannan matsalar, kuma gwamnati tana da shirin kawo sauƙi a nan gaba.”
Rahotanni sun nuna cewa wasu ƙauyuka a yankin Minjibir ma na fama da irin wannan matsalar ruwan sha, abin da ke tilasta wa mazauna yin doguwar tafiya domin neman ruwa, musamman a lokacin rani.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
