News
Kotu bata da ikon Tilasta Auren Mai Wushirya da ‘Yar Guda – Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Bar Association – NBA) ta bayyana damuwa kan rahotannin da ke cewa wata Kotun Majistare a Jihar Kano ta bayar da umarnin cewa a ɗaurawa fitattun masu amfani da TikTok, wato Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda aure cikin kwanaki 60, bayan wata shari’a da ta samo asali daga fitar da bidiyon da bai dace ba.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mazi Afam Osigwe SAN, shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA ya fitar a ranar Talata.
NBA ta bayyana cewa wannan mataki yana nuna rashin fahimtar iyakar ikon kotu bisa tsarin mulkin Najeriya, tare da zama mai take hakkin ɗan Adam.
Kungiyar ta jaddada cewa: “Babu wata kotu a Najeriya da take da ikon tilastawa mutum yin aure da wani, ko tilasta mutane biyu su yi aure dole. Wannan abu ya saɓawa tsarin mulki kuma ba baya a bisa ƙa’ida.”
A cewar ƙungiyar, aure a asali haɗin kai ne na son rai tsakanin waɗanda suka amince da juna, ba kuma za a taɓa iya tilasta shi a matsayin hukunci ko gyaran hali ba.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
