News
Kwamishinan Shari’a Na Kano Ya Halarci Taron Nahiyar Afrika Kan Yaƙi Da Safarar Mutane A Legas
Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude (SAN), na daga cikin manyan jami’an shari’a daga sassa daban-daban na nahiyar Afrika da suka halarci taron farko na nahiyar Afrika kan yaƙi da safarar mutane da tsafin sadaukarwa, wanda ake gudanarwa a Radisson Blu Hotel, da ke Ikeja, Legas.
Taron, wanda zai gudana daga Alhamis, 23 zuwa Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, na ɗauke da taken “Hadin Kan Afrika Wajen Yaƙi da Tsafin Sadaukarwa da Safarar Mutane.” Gwamnatin Jihar Legas ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Jami’ar Pepperdine University daga Malibu, California, Amurka.
Cutar Lassa Ta Yi Ajalin Mutum 172 A Bana A Najeriya— Hukumar NCDC
Manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin kai da musayar ƙwarewa tsakanin ƙasashen Afrika domin samar da ingantattun matakai da tsare-tsare na dindindin wajen magance matsalolin safarar mutane, tsafi da sauran laifukan da ke tauye mutuncin ɗan Adam a nahiyar.
Yayin da yake jawabi a wajen taron, Maude ya yaba wa Gwamnatin Jihar Legas bisa jagorancinta wajen shirya wannan gagarumin taro, yana mai cewa lokaci ya yi da ya kamata ƙasashen Afrika su ƙarfafa tsarin doka da gina cibiyoyin da za su kare waɗanda ke cikin haɗari, tare da tabbatar da adalci ga waɗanda suka tsira daga irin waɗannan mummunan laifuka.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, za ta ci gaba da tallafawa duk wani shiri da ke nufin kare martabar ɗan Adam da tabbatar da mulkin doka a cikin al’umma.
Taron Africa Colloquium 2025 na ɗaya daga cikin muhimman matakai da ake ganin za su ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Afrika wajen kawar da matsalolin safarar mutane da tsafin da ke cin zarafin ɗan Adam, tare da buɗe sabbin hanyoyi na haɗin gwiwar doka da tsaro a tsakanin ƙasashen nahiyar.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
