News
Hare-haren ’Yan Bindiga Ya Fara Ƙamari A Yankin Shanono, Jihar Kano
Mazauna ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano sun bayyana tsananin damuwa kan yadda ’yan bindiga ke ƙara kai hare-hare a yankin, suna kashe mutane, yin garkuwa da su da kuma satar dabbobi.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis a Kano, Yahaya Umar Bagobiri, shugaban Kwamitin Tsaron Faruruwa, ya ce al’ummar yankin na cikin halin tsoro tun daga shekarar 2022, lokacin da ’yan bindiga suka fara shigowa daga jihar Katsina domin kai hare-hare.
WAEC Ta Fara Gwajin Rubuta Rarrabawar ‘Essay’ Ta Kwamfuta Kafin 2026
Bagobiri ya bayyana cewa cikin ’yan watannin nan, ’yan bindigar sun sace akalla shanu 150, tare da kashe mutane da dama da kuma lalata gidaje da gonaki. Ya ƙara da cewa tun bayan barkewar hare-haren zuwa yanzu, fiye da shanu 1,600 da wasu kayayyaki aka sace, lamarin da ya tilasta wasu mazauna yankin tserewa zuwa jihar Katsina domin tsira da rayukansu.
Ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, su kawo dauki cikin gaggawa ta hanyar tura ƙarin jami’an tsaro da haɗa kai tsakanin sojoji da ’yan sanda domin dakile barazanar.
Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu, wasu kauyuka da ke yankin Faruruwa sun zama kufai, bayan da mazauna suka tsere saboda tsoron sake kai musu hari.
