News
“Idan Mijinki Baya Iya Kai Ki Awun Juna Biyu, To Ba Sonki Yake Ba” — Dr. Zainab Mu’azu
Wata likita daga sashen kula da lafiyar al’umma na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, Dr. Zainab Mu’azu, ta bayyana cewa babu soyayyar da ta fi kulawa da lafiyar mace, musamman a lokacin da take ɗauke da ciki.
Dr. Zainab ta faɗi hakan ne a yayin wata tattaunawa da ta yi da Albarka Radio Bauchi, inda ta ce idan har miji baya iya barin aikinsa domin ya raka matarsa awun Juna Biyu, ya tsaya har a gama sannan su koma gida tare, to hakan na nuna ba gaskiya yake ba, kuma baya son matar tasa.
“Idan mijinki baya iya barin aikin da yake yi, ya kai ki awun Juna Biyu, ya zauna a gama ku koma gida, to ki yi hakuri, ba gaskiya yake ba, baya sonki,” in ji ta.
Ta ce soyayya ba wai kalmomi ne kawai ba, illa dai a nuna ta cikin aikata abin da zai tabbatar da kulawa da juna.
“Miji da ke son matarsa, zai nuna hakan ta hanyar kulawa da lafiyarta da ta jaririn da take ɗauke da shi,” in ji ta.
Likitar ta kuma yi kira ga maza da su riƙa sadaukar da lokaci da kulawa wajen rakiyar matansu zuwa asibiti tun daga farkon lokacin ɗaukar Juna Biyu har zuwa lokacin haihuwa, tare da ci gaba da zuwa ganin likita da bin jadawalin rigakafi.
A cewarta, hakan ba wai taimako ba ne kawai, alhaki ne da kuma hujjar soyayya ta gaskiya.
