Connect with us

News

DSS Sun Cafke Wani Matashi Bisa Yin Kira Ga Sojoji Da Suyi Juyin Mulki A Shafin X

Published

on

Dss

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama wani mai amfani da kafar sada zumunta, Innocent Chukwuma, bisa zargin yin kira ga dakarun soji da su kifar da gwamnatin tarayya.

Chukwuma, wanda ke amfani da sunan @TheAgroman a shafin X, ana zarginsa da wallafa sakonni da ke kira ga sojoji su rusa jam’iyyar mai mulki tare da dakatar da gwamnatin kasar.

WAEC Ta Musanta Zargin Takaita Wa Dalibai Rubuta Wasu Darussa A Jarabawar 2026

Rahotanni sun ce jami’an DSS sun gano shi ne a yankin Oyigbo da ke birnin Port Harcourt na jihar Rivers, inda suka cafke shi bayan binciken da suka gudanar kan rubuce-rubucensa a shafin sada zumunta.

Hukumar ta ce matakin ya zama dole ne saboda irin kalaman da ake ganin na iya tayar da hankalin jama’a da kuma tada tarzoma a cikin kasa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jita a kafafen sada zumunta kan yiwuwar juyin mulki a Najeriya — lamarin da hukumomin tsaro suka bayyana cewa “babu gaskiya a ciki, kuma manufar shi ne tada hankalin al’umma.”

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending