News
Kogi Polytechnic Ta Dakatar Da Ma’aikata 5, Ta Kama Dalibai 4 Kan Magudin Takardun Karatu Na Jabu
Hukumar Kogi State Polytechnic da ke Lokoja ta ce tana gudanar da bincike kan wata ƙungiya da ake zargi da yin maguɗin takardun shaidar karatu da kuma jabun sakamako a cikin makarantar.
Rector na makarantar, Farfesa Salisu Ogbo, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake magana da manema labarai a Lokoja.
Ya ce an dakatar da ma’aikata biyar, yayin da aka kama dalibai hudu da ake zargin suna da hannu a cikin zancen.
Farfesan ya ce binciken farko ya gano takardun shaidar ND guda 30 da aka ƙirƙira kuma aka sayar da su ga wasu mutane da nufin neman shigar HND da su.
Ya ce an gano wannan maguɗin ne bayan rahotannin leƙen asiri da kuma binciken tantancewa da sassan Admission, ICT da na tsaro na makarantar suka gudanar.
A cewarsa, akwai wasu ma’aikatan da suka haɗa kai da masu sarrafa sakamako domin shirya sakamakon ƙarya ga daliban da suka kasa jarrabawa, amma ake nuna su kamar sun kammala karatu.
Farfesa Ogbo ya ce irin waɗannan ayyuka suna barazana ga martabar makarantar da amincin takardunta, yana mai jaddada cewa duk wanda aka tabbatar da laifinsa zai fuskanci hukunci.
“Ba za mu lamunci wani aiki da zai bata martabar wannan makaranta ba. Za mu ci gaba da kare sahihancin takardunmu,” in ji Farfesa Ogbo.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
