Connect with us

News

Jirgin Ƙasa Ya Faɗi Kwanaki 4 Kacal Bayan An Shafe Watanni Ana Gyare-gyare A Najeriya  ‎

Published

on

images 23 1

Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC) ta sake dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a layin Warri–Itakpe, bayan wani hatsari da ya faru da yammacin Asabar, inda wasu daga cikin tirelolin jirgin suka faɗi.

‎Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, a daidai kilomita 212+8m da ke kusa da Agbor, a Jihar Delta. Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu kacal bayan an dawo da zirga-zirgar jiragen a layin, bayan watanni ana gyare-gyare.

Shugaba Tinubu Zai Gana Da Trump Kan Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya 

‎Layin Warri–Itakpe, wanda ke da tsawon sama da kilomita 300, yana ɗaya daga cikin manyan sabbin layukan jirgin ƙasa na zamani a Najeriya, bayan na Lagos–Ibadan da Abuja–Kaduna.

‎Shugaban hukumar NRC, Injiniya Kayode Opeifa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce binciken farko ya nuna cewa lalata layin dogo (track vandalism) ne ake zargi da haddasa hatsarin.

‎A cewarsa, “Dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin an kwashe su lafiya zuwa Agbor, kuma babu wanda ya ji rauni.”

‎Hukumar ta ce an fara bincike don gano musabbabin lamarin da kuma waɗanda ke da hannu a cikin yiwuwar lalata layin.

Advertisement

‎Sai dai har yanzu NRC ba ta bayyana lokacin da za a sake dawo da zirga-zirgar jiragen a layin ba.

 

PLATINUM POST NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending