News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekaru 71 Bisa Zargin Kashe Matarsa Mai Shekaru 67
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke tsoho, Jeriel Clifford Peter, mai shekaru 71, bisa zargin kashe matarsa, Miltha Jeriel, mai shekaru 67, a ƙaramar hukumar Demsa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Sulaiman Nguroje, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 6 ga Nuwamba, 2025, bayan wata sabani a wani mashaya da ya rikide zuwa tashin hankali.
An Ceto Mutum 221 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Jigawa — NAPTIP
Nguroje ya ce wanda ake zargi ya yi amfani da wuka wajan farmakar matarsa . An garzaya da ita asibiti amma ta rasu yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarta. Gawarta an ajiye a ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da bincike.
‘Yan sanda sun kama tsohon nan take, tare da kwato kayan da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Dankombo Morris, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin imani da tausayi, sannan ya umurci Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Yola su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.
