News
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 5 Ciki Har Da Masu Shayarwa A Kano
’Yan bindiga sun kai mummunan farmaki a ƙauyen Yan Kwada, da ke yankin Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka sace mata biyar, ciki har da masu shayar da jarirai.
Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne a yammacin Lahadi, lokacin da maharan suka shiga ƙauyen da yawan gaske, ɗauke da muggan makamai, suna harbe-harbe ba ji ba gani.
Dalilin Da Ya Sa Jihar Kano Ke Duba Yiwuwar Amfani Da Harshen Hausa Wajen Koyarwa A Makarantu
“Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi tare da fasa ƙofofi. Sun ɗauki mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaye sunansa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mata biyu daga cikin waɗanda aka sace sun samu kuɓuta, yayin da uku ke ci gaba da kasancewa a hannun ’yan bindigar.
Wannan harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan da dakarun soji suka yi artabu da ’yan bindiga a yankin, inda suka hallaka 19 daga cikinsu a wani samame na haɗin gwiwa.
Duk da hakan, hare-haren na ci gaba da haifar da fargaba a yankunan iyakar Kano da Katsina, inda al’umma ke rayuwa cikin tsoro.
Mazauna yankin sun ce ƙauyuka da dama sun zama kufai, yayin da wasu ke ƙauracewa zuwa garuruwan da ke kusa ko manyan birane domin neman mafaka.
Mahukunta dai har yanzu ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da al’umma ke ci gaba da kira ga hukumomi da su ƙara ƙarfin tsaro a yankin.
